<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>32</hymn_number>
<title>Ya Al'ummai, Ku Ɗaukaka Allah A Naku Zukata LW32</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Al'ummai, ku ɗaukaka
 Allah a naku zukata.
 Ku bauta wa Madauwami,
 Ku yabe shi da rerawa.

[V2]
 2) Ubangiji shi Allah ne,
 Mahalicci sahihi kuwa.
 Ya mai da mu mutanensa,
 Tumakin makiyayarsa.

[V3]
 3) Ku shiga cikin ƙofarsa,
 Da yabo shiga gidansa,
 Ku gode domin jinƙansa,
 Albarkaci sunansa kuwa.

[V4]
 4) Ubangiji kyakkyawa ne,
 Jinƙansa babu iyaka,
 Amincinsa ya tabbata
 Tun zamanai, har abada.</lyrics>
</song>